Yadda gwamnatin Ganduje ke shirin nakasta dubban ɗalibai a ɓangaren Ilimi

335

Sama da ɗalibai dubu 80 ke cikin barazanar rasa gurbin karatu a makarantun gaba da sakandare sakamakon maƙalewar jarrabawarsu ta NECO, da gwamnatin jihar ba ta biya bashin da ke kanta ba.

Wannan yanayi da ɗaliban suka tsinci kansu na da alaƙa da gazawar gwamnatin jihar na biyan kuɗaɗen da hukumar shirya jarrabawar kammala sakandare ta Najeriya wato NECO ke binta.

Kashi 70 cikin 100 na ɗaliban da suka rubuta jarrabawar ta shekarar 2021, iyayensu ne suka biya musu kuɗin jarrabawar, amma har yanzu babu labarin sakin jarrabawar tasu.

Wannan yanayi da ɗaliban ke ciki ya ja hankali abin da ya kai ga ƙungiyoyin masu fafutika jan hankalin gwamnati don ganin yaran ba su rasa damar ci gaba da karatu a wannan zangon ba.

Wasu rahotanni na cewa hukumar NECO na bin gwamnatin Kano sama da naira miliyan 500, duk da cewa a makon da ya gabata gwamnati ta shaida cewa ta rage bashin da ake binta da naira miliyan 100.

Gwamnatin Kano ta alaƙanta yawan bashin da NECO ke binta da matsalolin matsin tattalin arziki da kuma rashin kuɗaɗen shiga.

Wannan ba shi ne karon farko da ɗaliban jihar Kano ke shiga cikin irin wannan yanayi ba, domin kusan kowacce shekara ba a rasa irin wannan korafi na rike jarrabawar ɗaliban saboda bashi.

A watan Afrilu ma an samu ɗalibai dubu 20 da suka rubuta jarrabawar kammala sakandare ta Arabiya da ta fasaha da aka rike jarrabawarsu kan bashi.

Haka kuma a shekarar da ta gabata, sai da aka rike wa ɗaliban jihar sama da dubu 70 sakamakon jarrabawarsu har sai da aka biya NECO bashin da take bi na sama da naira miliyan 640.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan