‘Yan Najeriya Miliyan 15 Na Shan Miyagun Ƙwayoyi— NDLEA
Shugaban Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya, NDLEA, Buba Marwa, ya ce ‘yan Najeriya miliyan 15 ne suke shan miyagun ƙwayoyi.
Buba ya bayyana haka ne a yayin wani taron tattaunawa da shugabannin ƙananan hukumomi ranar Laraba a Jos.
Ya nuna damuwa bisa yadda ake rarraba tare da shan miyagun ƙwayoyi a ƙasar nan, yana mai ƙarawa da cewa mutum ɗaya daga cikin bakwai na ‘yan Najeriya na shan miyagun ƙwayoyi.
Ya bayyana wannan al’ada a matsayin “abin kunya”, yana mai cewa hukumar ta tanadi matakan da za ta kawo ƙarshen wannan mummunar ɗabi’a.
Ya ce shan miyagun ƙwayoyi ya hallaka matasa da al’umomi da yawa, abin da ya tilasta hukumar ta kira wannan taro.
“Maganar da nake da ku yanzu, ‘yan Najeriya miliyan 15 na sha muggan ƙwayoyi; ɗaya daga cikin ‘yan Najeriya bakwai na shan muggan ƙwayoyi.
“Ba wani gari a Najeriya da ba a shan ƙwaya, kuma haka ne ya sa muke ci gaba da samun ƙalubalen tsaro”, in ji shi.