Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya Femi Gbajabiamila ya shiga tsakani a tattaunawa tsakanin gwamnati da ƙungiyar ASUU ta malaman jami’o’i, inda ya sasanta su.
Zaman sasantawar ya biyo bayan barazanar da ASUU ta yi na sake shiga yajin aiki idan gwamnatin ba ta cika alƙawarin da aka yi a yarjejeniyoyi tsakaninsu ba.
Yayin zaman wanda ministocin ilimi da na kuɗi suka halarta, ɓangarorin biyu sun amince da abu huɗu kamar haka:
- Gwamnati za ta biya malaman jami’a naira biliyan 30 cikin mako ɗaya a matsayin kuɗin farfaɗo da jami’o’in
- Gwamnati za ta fitar da biliyan 22 a matsayin alawus na malaman daga kasafin kuɗin ma’aikatar ilimi
- Gwamnati ba za ta ƙi yin amfani da tsarin biyan albashi ba na UTAS wanda ASUU ta samar maimakon IPPIS na gwamnati
- An amince a ganawar cewa yarjejeniyar naira tiriliyan 1,3 da aka cimma a 2009 za ta fara aiki cikin mako ɗaya mai zuwa
Ministar Kuɗi Zainab Ahmed ta bayyana cewa gwamnati na jiran rahoton kwamatin hukumar cigaban kimiyya da sadarwa ta NITDA kafin aiwatar da matakan da aka cimma.
“Abin kunya ne a matsayinmu na shugabanni mu zuba ido yayin da abubuwa ke lalacewa,” in ji Mista Gbajabiamila.
Turawa Abokai