Majalisar Tattalin arziki ta ƙasa, NEC ta baiyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya sahale da a fitar da Naira biliyan 656 a matsayin wani tallafi ga jihohin ƙasar nan 36.
Zainab Ahmed, Ministar Tattalin Arziki, Kasafin Kuɗi da tsare-tsare ce ta baiyana hakan a taron majalisar zartaswa ta ƙasa da a ka yi ta yanar gizo ran Alhamis.
Ministar ta ce tallafin bashin zai taimakawa jihohin su biya wasu buƙatunsu na kuɗaɗe, musamman ma wajen kasafin kuɗi.
Ta ce ko wacce jiha za ta samu Naira biliyan 18.2, inda ta ƙara da cewa Babban Bankin Ƙasa, CBN ne ya ke shirye-shiryen fitar da maƙudan kuɗaɗen.
“Za a kwashe watanni shida a na rabon kuɗin amma a rukuni shida za a raba ,ba wani farar-daya ba.
“Ana sa ran ko wacce jiha za ta samu adadin biliyan 18.225 na bashin, kuma sai nan da shekaru biyu za a fara biya sannan za a kwashe shekaru talatin a na biyan kuɗin. Za kuma a riƙa biyan kuɗin ruwa na kashi 9 na kuɗin,” in ji ministar.