Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya biya fitaccen ɗan jaridar nan mawallafin jaridar Intanet, Daily Nigerian, Jaafar Jaafar, naira N800,000.
Jaafar Jaafar ya shaida wa Freedom Radio Kano cewa Gwamna Ganduje ya biya wannan kuɗi kamar yadda kotu ta umarce shi.
Haka kuma Jaafar ya wallafa wani rubutu a shafinsa na Facebook, inda ya ce: Alert ya shigo. Ku tafa wa na Gwaggo.
A watan Yuli, 2021, Babbar Kotun Jihar Kano, Bompai, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Baba Na Malam ta umarci Gwamna Ganduje ya biya Jaafar Jaafar wannan kuɗi sakamakon ɓata masa lokaci a wajen shari’ar faifan dala.
Tun a 2017 ne Jaafar Jaafar ya wallafa wasu faya-fayan bidiyo, inda aka ga Gwamna Ganduje na sa dalolin Amurka a aljihu a matsayin cin hanci.
Sakamakon haka ne ya sa Gwamna Ganduje ya maka Jaafar Jaafar a kotu, yana mai cewa ɗan jaridar ya ɓata masa suna.
A watan Mayu, 2021, Jaafar Jaafar ya fice daga Najeriya zuwa Landan bayan da ya zargi Gwamna Ganduje da yi masa barazana da rayuwarsa.