Namijin Duniya: Yadda wan ɗan ‘Bojuwa’ ya angwance da mata 9 lokaci guda a ƙasar Brazil

824

Wani fitaccen mai tallan kaya a Brazil, Arthur O Urso ya auri mata 9 farar-ɗaya .

Urso ya yi auren kece-rainin ne domin ya yaɗa aƙidar cewa soyayya ta kowa da kowa ce sannan kuma ya yaƙi auren mace ɗaya tak.

An ɗaura auren a cocin katolika da ke birnin Sao Paulo.

Tun da fari da Urso na auren Luana Kazaki ne ita kaɗai, amma da su ka tafi yawon shaƙatawa, sai su ka yanke shawarar ya ƙaro wasu matan guda 9 rigis domin nuna cewa soyayya ta kowa da kowa ce.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan