Bayan Zargin Fataucin Miyagun Ƙwayoyi: Zainab Aliyu Kila ta zama jami’a a hukumar NDLEA

773

Matashiyar nan da Gwamnatin ƙasar Saudiyya ta kama a cikin Disamban shekarar 2018 lokacin da ta je kasar tare da mahaifiyarta da ‘yar uwarta domin gudanar da aikin Umrah, Zainab Aliyu Kila, bisa zargin fataucin miyagun ƙwayoyi ta zama jami’a a hukumar da ke hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA).

Tun da farko jami’an tsaron ƙasar Saudiyya sun zarge ta da safarar ƙwayar Tramadol har guda 2,000 bayan da aka ga kwayoyin a wata jaka mai dauke da sunanta.

Zainab Aliyu Kila

Sai dai daga baya da aka zurfafa bincike hukumar yaki da ta’ammali da miyagun kwayoyi ta NDLEA ta gano cewa wasu ma’aikata ne a filin jirgin saman Malam Aminu Kano suka saka mata kwayar a jakarta.

Bayan kammala karatu a jami’ar Yusuf Maitama Sule da ke Kano, ta samu nasarar shiga jerin sababbin ma’aikatan da hukumar yaki da ta’ammali da miyagun kwayoyi ta NDLEA a matsayin babbar jami’a wato Narcotic Officer.

Zainab tare da iyayenta

Tuni dai shafukan sadarwa na zamani musamman shafin Facebook, su ka cika da hotunan matashiyar wacce yar asalin jihar Jigawa ce da ke zaune a birnin Kano.

A lokacin haɗa wannan rahoton wakilin Labarai24 ya yi kokarin jin ta bakinta akan wannan sauyi da ya sameta, amma bai samu nasarar samunta ba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan