Shugaban bangaren gwamnati na jam’iyyar APC Alhaji Abdullahi Abbas ya yi bayani cewa jam’iyyar APC ta saiwa Mallam Ibrahim Shekarau fom din takarar kujerar Sanata akan kudi naira miliyan bakwai, kuma ta yi masa talla, ta bashi gudunmawa, sannan ta tallafa masa.
WANNAN HAKA YAKE a duk jihar Kano shi kadai ne aka bashi kyautar fom, aka je har gidansa aka yi masa mubayi’a : AMMA KUMA:
GA dalilai bakwai da suka sanya a wannan lokacin na shekarar 2018-2019 aka yi haka:
Na daya: Shekarau dan siyasa ne, mai daraja da jama’a, sannan mai mutunci da za a iya rabewa da shi a yi nasara.
Na biyu : Siyasar Kano gida uku ce, tsagin Madugun Kwankwasiyya da bangaren masoya da mabiya tsarin Sardaunan Kano, sai kuma masu biyayya ga duk abin da gwamnati ta zo da shi, wato ‘yan Establishment. Ana son gida biyu su hadu guri guda.

Na uku: Da aka baiwa Shekarau fom na miliyan bakwai kyauta, an bashi don ya zagaya kananan hukumomi 44 ya yi kamfen. Ya halarci tarukan siyasa na yada angizon APC, ya yi hirarraki a kafafen yada labarai, sannan ya bada shawarwari da dabaru da irin nasa experience don a samu nasara.
Na hudu: A yi kwalliya da shi, a yi amfani da kwarjininsa da haibarsa. Ya yi gwamna, ya yi minista kuma ma’aikata da ‘yan fansho, da masu ra’ayin addini da ‘yan dimokudiyya da siyasar tsabta da masu dangwale da ‘yan kasuwa da mata da talakawa da saraki suna kaunarsa.
Na biyar dana shida da na bakwai, Sanata Mallam Ibrahim Shekarau an roke shi, an gayyace shi, an rarrashe shi, an kai gwauro an kai mari, an yi godo a Kaduna da Abuja da Lagos da Kano a Mundubawa don ya shigo ya bada gudunmawarsa. Ya karba, ya shiga kuma ya yi hidima.
Menene laifi kuma menene abin suka, Ya kai Abdullahi Abbas!!!
Bello Muhammad Sharada,hadimi ne ga Sanata Malam Ibrahim Shekarau akan harkokin kafafen yada labarai, ya rubuto daga Kano