Illar Shayen – shayen Miyagun Ƙwayoyi A Tsakankanin Matasa A Najeriya

    250

    Wannan tashin hankalin da ke faruwa a kudancin Najeriya shi ne yaduwar abin sa mayen da ake kira Meth wanda a duk cikin ababen sa maye babu wanda ya kai wannan jaraba. Tsorona kada mu ma ya mamaye mu a Arewacin Najeriya.

    Domin shi ne kololuwa a duk wani abin sa maye. Haka kuma duk wanda ya fara shan sa da wuya ya daina saboda jin dadin da suke samu a cikinshi.

    Amma babu abin da ya kai shi saurin lalata maka lafiya da rayuwarka gaba daya kamar wannan jarabar.

    Ko da wasa kada ka dandana domin idan ka dandana ka sadakar da rayuwarka kenan gare ta sai kuma yadda ta yi da kai.

    Idan ta yi kira dole ka amsa. Ka jera kwanaki ba ka yi bacci ba. Rashin bacci kuma hauka ya ke sa mutum.

    Mutum zai iya halaka duk wanda ya so ya shiga tsakaninshi da wannan jarabar.

    Ko da ka yi sa’a ka bar ta, har ka koma ga Allah ba za ka taba daina tunaninta ba, a cewar wani da ya Allah Ya taimake shi ya daina.

    Kuma wai sai aka dauki matakin zane duk wani da aka kama yana amfani da shi. Mutumin da ya nisa a cikin wannan harkar, me duka zai yi masa? Mai sauran hankali ne zai fahimci wannan.

    Gaskiya dole a tashi tsaye wajen samar da wuraren farfado da mutanen da suka fada tarkon shaye-shaye.

    Daga shafin Facebook na Maryam Bugaje

    Turawa Abokai

    RUBUTA AMSA

    Rubuta ra'ayinka
    Rubuta Sunanka a nan