Ko kun san Sarkin da ya ke shanye karan sigari 225 a rana guda?

413

Tsohon Sarkin ƙasar Albania mai suna Ahmet Muhtar Zogolli, a lokacin yana duniya yana shanye karan sigari 225 a rana ɗaya.

Haka kuma a lokacin rayuwar wannan Sarki da ake masa laƙabi da Sarki Zog I ya tsallake hare – hare daga masu son su hallaka shi har sau 55.

Sarki Ahmet Muhtar Zogolli

Tarihi ya bayyana cewa an taɓa naɗa Sarki Zogi I shugaban masu zukar taba na duniya a shekarar 1923.

Hakazalika Sarki Zogi I ya rayu tsakanin shekarun 1895 zuwa ranar 9 ga watan Afrilun 1961.

Kasar Albania dai tana yankin Balkan a kudu maso gabashin nahiyar turai.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan