Na hango wanda zai zama shugaban ƙasar Najeriya a 2023 – IBB

1148

Tsohon shugaban ƙasar Najeriya na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya bayyana cewar tuni ya hango wanda zai gaji buzun kujerar shugaba Buhari a kakar zaɓe ta 2023.

IBB ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da akayi da shi a gidan TV na Arise TV.

“Naga wani matashi da shekarunsa basu wuce 60 ba ya ɗare kujerar shugaban ƙasar Najeriya a 2023, kuma wannan matashi ya haɗa duk wata cancanta da nagarta da Najeriya ke buƙata idan har aka bashi damar tsayawa.” Inji IBB.

Ibrahim Badamasi Babangida

“Ina shawartar ƴan Najeriya da kada su sake su zaɓi mutumin da ya haura shekaru 60 a matsayin shugaban ƙasa.”

“Halin da Najeriya take ciki a yanzu tana buƙatar jagorancin matashi mai ƙwarewa a fannin tattalin arziki da iya siyasa, wanda yake da abokai a dukkan sassan ƙasar nan, wanda ya iya tafiyar da al’umma.” Inji shi

Shin ko wa kuke hasashen tsohon shugaban ƙasa IBB na magana a kansa?

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan