Wasu hotuna da jaridar Sahelian Times ta wallafa a shafinta ya nuna yadda wasu matasa ɗauke da kwalaye da aka yi rubuce-rubuce da su ke kira ga kakakin majalisar Najeriya da ya kori ɗan majalisar mai wakiltar ƙaramar hukumar Birnin Kano da Kewaye daga shugaban kwamitin tsaro na zauren majalisar.

Matasan sun yi wannan zanga – zangar ne a yau Asabar akan hanyar shiga gurin da ake zaman makokin mataimakin shugaban rukunin kamfanin Dangote, Alhaji Sani Dangote da ya rasu a makon jiya.

Haka kuma matasan sun shirya zanga-zangr ne a dai-dai lokacin da tawagar kakakin majalisar wakilan Najeriya, Femi Gbajabiamila ke ƙoƙarin isa ga gurin zaman makokin domin ta’aziyya.

Rikicin siyasa dai tsakanin shugaban ƙaramar hukumar Birnin Kano Fa’izu Alfindiki da ke goyon bayan shugabancin Abdullahi Abbas Sanusi a matsayin shugaban APC da kuma ɗan majalisar tarayya Sha’aban Ibrahim Sharada da ke adawa ya yi ƙamari a ɗan tsakanin nan, la’akari da yadda Fa’izu Alfindikin ya jagoranci rushe wata cibiyar koyar da matasa sana’o’i a unguwar Sharada da Sha’aban ɗin ya ke ginawa.