Fitaccen ɗan Jaridar nan na gidan rediyon Freedom a Kano, Ibrahim Ishaq Danuwa Rano ya bayar da shawarar yadda ya kamata a raba kuɗin mawaƙi Davido naira miliyan 250 da ya ce ya bayar da su kyauta domin tallafawa gidajen marayu a Najeriya.
Ibrahim Danuwa Rano, wanda shi ne ke gabatar da shirin siyasa na ‘Kowanne Gauta’ ya bayyana hakan ne a yau Asabar a shafinsa na facebook, inda mutane da dama su ka bayyana ra’ayinsu akan wannan batu.
“Aƙalla idan aka ɗauki gidajen Marayu goma a kowacce jiha dake faɗin Najeriya, za su iya amfana da kayan abinci ko zallar kuɗi da ya tasamma kusan Naira dubu ɗari bakwai, daga cikin Naira Miliyan ɗari biyu da hamsin da fitaccen mawaƙin nan Davido ya shirya miƙa su ga masu rangwamen gata“
Ya ƙara da cewa “Idan bamu manta ba, Mawaƙi Davido ya tara kuɗaɗen ne ta hanyar neman gudunmowa daga ƴan uwa da abokanan arziƙi domin ta ya shi murnar ƙarin shekara, kuma bayan gudunmawar ta kai kimanin Naira Miliyan ɗari biyu, shi ma ya ce ya ƙara miliyan hamsin daga aljihunsa, tare da kafa kwamitin nagartattun mutane da za su yi aikin raba kuɗaɗen ga gidajen marayu a dukka jihohin Najeriya” In ji Ibrahim Danuwa Rano.

Haka kuma ɗan jaridar ya yi addu’ar Allah ya sa ma su hali su yi koyi da wannan halin karamci da mawaƙin ya yi.
“Domin zuciyar taimako, Davido ya ce duk shekara zai yi irin wannan asusun domin tallafawa mabuƙata. Ka ji ruhin tausayi Mallam. Allah ka sa Davido ya musulunta, kuma Allah ka sa dukkan musulmi mu yi koyi da hali irin nasa na tausayin marasa ƙarfi“
Idan za a iya tunawa dai a yau ne mawaki Davido ya ce ya kyautar da naira miliyan 250 domin tallafa wa gidajen marayu a Najeriya. Mawakin ya ce ya samu kyautar naira miliyan 200 cikin kwana biyu bayan da ya nemi a ba shi gudunmuwar bikin ranar haihuwarsa, sai shi kuma ya kara naira miliyan 50 a kai kuma ya kyautar da su ga marayu.