Ranar Alhamis 20 ga watan Nuwamba ce ranar yara ta duniya da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe da nufin jawo hankalin kasashen duniya akan halin da yara ƙanana ke ciki.
Haka kuma domin yin waiwaye kan halin da yaran ke ciki a sassan duniya daban-daban.
Yara dai a ƙasashe masu tasowa kamar Najeriya dai na fama da matsalolin rayuwa da dama, kama daga yawan fyade daga manya, zuwa fatauci da kuma safararsu musamman a kudancin ƙasar nan.
Wani rahoto da asusun tallafawa kananan yara na Majalisar dinkin duniya UNICEF, ya fitar na nuni da cewa ana azabtar da miliyoyin yara ko yin lalata da su a duniya. Asusun ya ce ana bautar da yara kimanin miliyan 200 a duniya baki ɗaya yayin da a duk shekara masu fataucin bil Adama na sace yara miliyan daya da dubu 200. Hakan kuwa na faruwa ne duk da ƙkudurin kare ´yancin yara na MƊD wanda ƙasashen duniya suka sanyawa hannu.
Wanene yaro da haƙƙoƙinsa?
Yaro shi ne mutumin da yake daga shekara ɗaya zuwa 14 sai kuma ɗan matashi daga 14 zuwa 17 a yadda dokokin ƙasa da ƙasa suka fassara.
Dokokin ƙasa da ƙasa sun bayyana cewa dole kula da yara sun haɗa da yin duk wani abu don ci gabansu a zahiri da tarbiyya da cinsu da shansu da kula da iliminsu (mai kyau) da lafiyarsu da walwalarsa.

Sannan dokokin sun haramta dukan yaro ko yaya yake, amma dokokin Afrika ba su hana dukan yaro ba, ”sai dai dukan ka da ya zama wanda zai yi masa lahani.
Haka kuma Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya Unicef ya ce a kan ci zarafin yara a gidaje ko a cikin danginsu ko makarantu ko unguwanni da cikin al’ummomi da ma sauran wuraren da ake sa ran yaran z su kasance cikin aminci
Hanyoyin cin zarafin yara sun haɗa da:
- Dukansu ko ƙona su ko yi musu wani lahani a jiki ko yin jifa da su ko sanya musu guba ko ɗaure su.
- Cin zarafinsu ta hanyar lalata da su ko tattaɓa wasu ɓangarori na jikinsu da nufi a ji daɗi.
- Cin zarafin su ta hanyar takurawa ko razanarwa ko cuzgunawa ko tsoratar da su.
- Yin watsi da su ta hanyar banztar da su a hana su abinci ko sutura ko muhalli.
A cikin shekarar 2003, Najeriya ta amince da dokar kare hakkin kananan yara wanda zai yi duba da kuma mutunta sharrudan dokoki da aka shimfida da zai kare su, sai dai ya zuwa yanzu jihohi 21 ne kadai cikin 36 har da babban birnin tarayyar kasar su ka ƙaddamar da wannan doka.

Wani rahoton bincike na duniya kan rayuwar yara, ya bayyana cewa, ana cin zarafin daya daga cikin yara hudu a duk fadin duniya, wajen sanya tsaiko a lokutan da ya kamata su yi amfani da shi don samun ilimi, girma da kuma walwala tsakanin ‘yan ’uwansu yara.
Hakazalika masana sun kiyasta cewa yara sama da miliyan 30 a yankin kudu da hamadar Sahara ba sa zuwa makaranta, kuma kashi 54 cikin 100 na yaran mata ne, lamarin da ya fi tsananta a Najeriya.