Tsohon babban limamin masallacin Ka’aba, Sheikh Adil Alkalbany, ya bayyana a wani sabon faifan bidiyo tare da wasu yan wasa inda suka yi wani shirin fim mai salon talla.
Sheikh Kalbany dai tuni ya bayyana aniyarsa ta shiga masana’antar Hollywood inda yake cewa ya dace da sana’ar fim bayan wasu sun ce bai dace ya bayyana a faifan ba.

Idan ba a manta ba dama wani dan wasan Kannywood ya taba cewa sana’ar fim tafi ta malinta fadakarwa. Watakila shi ma Sheikh Kalbani abin da ya lura da shi kenan.
Malamin dama ya saba bayyana a abubuwa masu tayar da hazo inda aka taba ganinsa a gurin wasan karta a shekarun baya.
A da’awar malamin dole addinin musulinci ya canja salo domin canja hanyoyin dakile tsattsauran ra’ayi da yake janyo masa ta’addanci.
Turawa Abokai