A aikace, tsakanin Bahaushe, Bayarabe da Inyamuri wa ya fi so a raba Najeriya ne?

440

Duba da yadda Inyamurai suke kasa saka jari a kasar da suke kira kasarsu ya sanya min kokwanton anya da gaske suke yi suna son kafa kasar tasu? Idan ka dubi yadda suka hada karfi da karfe a musamman Lagos da Abuja da Kano. Suka zuba jari na trillions yayin da zai yi wuya ka samu Inyamurin da ya sanya jarin sama da miliyan dari zuwa dari biyu a kasar da yake kira Kasarsa, saboda fargabar makomar kasar ya sanya ina shakkar idan Inyamuri da gaske yake yi maganar neman ‘yanci. Idan da gaske suke yi me yasa suka tafi suke ta raya wasu bangarori na kasar da ba bangarensu ba. Gaskiya akwai wasan kwaikwayo a cikin lamarin.

Shi kuma Bayarabe ya fi kowa morar Najeriya, Ya fi kowa yawa a ma’aikatan tarrayar Najeriya, ya fi kowa yawan kamfuna da sana’o’i. Idan aka ce a ware wa za su sayarwa da kayan da suke sarrafawa? Idan aka yi kasar Yarbawa hatta gabar teku dake kawo musu mahaukatan kudi na shipping sai ta girgiza. Don kuwa za a barsu ne da tsiyarsu kowa ya nemi mafita.

Malam Bahaushe bai furta da baki yana so a rabe ba, amma duba da halin ko’in kula dinsa ga kasar, kamar shi ya fi kowane dan Najeriya yin shakulatin bangaro da kasancewar Najeriya din a matsayin kasa daya. Kafin zuwan Usman Danfodio Bahaushe bai yarda da kasa ba, kowa garinsa shi ne kasarsa. Har yanzu Bahaushe bai sauya ba. In da za a ce a koma gidan jiya kowacce jiha ta koma matsayinta na asali gaskiya da Bahaushe zai fi so. Idan aka ce a dawo da Trans-Sahara-Route babu abin da zai dami Bahaushe. Idan ka ga Bahaushen dake son Najeriya ta cigaba da zama a matsayin kasa daya to tsirarin ‘yan siyasa ne da manyan masu mukamai da suke tatsar kasar kamar hauka. Idan muka dauke masu kudi irin Dangwate da Abdussamadu da suka yi karfi a wasu bangare na kasar nan. Bahaushe ya fi so ya zuba jarinsa a kasar hausa.

Duba da wannan hujjojin, ni a hangena Bahaushe yafi kowane Dan Najeriya son a raba Najeriya, a aikace ba wai a zance da hayagaga ba.

Bala Anas Babinlata marubuci ne ya rubuto daga Kano

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan