A duba hanyar Dr Ahmad Gumi wajen magance ta’addancin ƴan fashin daji

  236

  Idan mutum ba shi da lafiya ba magani daya yake sha ba, magunguna daban-dabam yake gwadawa har ya samu wanda zai masa magani. Haka nan idan mutum, ko al’umma, ta samu kanta a cikin wata matsala to ba hanya daya ake bi ba wajen shawo kan matsalar, ana gwada hanyoyi da yawa ne don neman waraka, musamman idan matsalar ta zama mai sassarkiya ce kamar matsalar tsaro da muke fama da ita a yau.

  Saboda haka, amfani da karfin soji kawai wajen magance matsalar tsaron da yan fashin daji suka haifar ba hikima ba ne. Hikima shi ne a gwada hanyoyi daban-dabam a lokaci guda, ana cizawa ana hurawa. Yawancin manyan yake-yake da kanana a tarihi ta wannan hanya ne aka magance su.

  Dr Ahmad Abubakar Mahmud Gumi na daga cikin yan Nijeriya da suka gabatar da shawarwari na yadda za a shawo kan wannan matsala ta hanyar ruwan sanyi. Dr baya a kan magana ba ne kawai, a’a ya shiga aiki ba ji ba gani don dabbaqa hanyarsa a aikace. Ya sadaukar da kansa, sadaukarwa irin wacce babu wani dan Nijeriya da ya yi irinta, ya kutsa cikin daji, ya iske yan fashin dajin nan a cikin dajinsu, kuma ya ji ta bakinsu. A karon farko, kuma a dalilin sadaukarwa da jarumta ta Dr Ahmad Gumi, yan Nijeriya sun ji daga bakin yan ta’addar nan me yake damun su, me ya sa suke kaddamar da ayyukan ta’addanci a kan yan uwansu.

  Kutsawar Dr Ahmad Gumi cikin daji da samun karba daga wadannan yan fashin daji cikin karamci da girmamawa, akalla ya nuna mana cewa mutanen masu hankali ne, kuma sun san abinda suke yi. Har yau, hakan ya nuna mana cewa, mutanen a shirye suke su karbi hannun abota da lalama idan aka mika musu shi. Mun ga yadda suka karbi littafan addini da Dr Gumi ya ba su cikin shauki da godiya, inda suka nuna cewa a shirye suke su rungumi zaman lafiya da rayuwa irin ta mutane idan al’umma ta saurare su, ta ji kokensu. Kamar yadda suka nuna cikakkiyar amincewa da Dr Ahmad Gumi da yarda da ya zama mai shiga tsakani a tsakaninsu da hukuma da kuma jama’ar gari. Wannan babban ci gaba ne wanda ya kamata a gina a kansa. A takaice yan fashin daji sun yarda da hanyar da Dr Gumi ya dauko, saura Gwamnati da jama’ar kasa su yarda da ita. Idan haka ta samu, to mun kama hanyar warware wannan matsala.

  Amma wacece wannan hanya ta Ahmad Gumi? Wannan hanya a takaice tana nufin hannunka ba zai rube ka yanke ka yar ba. Wadannan yan ta’adda yan uwanmu ne, duk da wannan mummunar barna da suke mana ta kashe-kashe da barnata dukiya da keta alfarma. Duk da haka yan uwanmu ne. Abinda suke mana yana da ciwo, amma hakan ba zai canja hakikanin cewa su yan uwanmu ba ne. Idan hannunka ya rube zai yi maka ciwo da wari da miki, tana yiwuwa ba za ka so ka dube shi ba saboda muninsa, amma kome ya zama hannunka ne, kuma da ka yanke shi ka yar gara ka yi masa magani.

  Kuma dole mu duba cewa tana yiwuwa hannun nan namu da ya rube laifinmu ne, wato a matsayinmu na al’umma. Mu duba dalilan da suka mayar da yan uwan nan namu yan ta’adda. Mun sani babu mutumin da uwarsa take haihuwar sa a dan ta’adda. A addinance ma mun sani cewa dukkanin abin haihuwa ana haihuwar sa a kan fidira, sai daga baya ya karkace ga barin fidirar. Bincike na ilmi ya nuna cewa, daga dalilan da suke mai da mutum dan ta’adda akwai zalunci da jahilci da talauci. Babu shakka wadannan abubuwa guda uku duka muna fama da su a yau a Nijeriya, kuma wadanda suka fi fama da su su ne mazauna karkara, a mazauna karkarar ma babu kamar Fulani makiyaya wadanda ko a karkarar ba sa zaune waje daya.

  A tunanin Dr Ahmad Gumi yan fashin daji yan uwanmu ne muka bari suka lalace. Mun bar su a cikin jahilci kuma wannan jahilci ya sa suka fuskanci zalunci daga bangarori daban-dabam, ciki har da zaluntarsu a dukiyarsu wanda hakan ya gadar musu da talauci. Wannan kuma daga bisani shi ya mayar da su yan ta’adda.

  Yana da kyau mu fahimci cewa wannan ba yana nufin daurin gindi ga Fulani da sauran ma duk masu fashin daji ba. A’a abinda yake nufi shi ne kokarin fahimtar matsalar a ilmance. Wanda kuma shi zai taimaka a warware matsalar a cikin ruwan sanyi.

  Ga alama hanyar Gwamnati ta kokarin magance matsalar tsaro da karfin soja ta gaza biyan bukata. Har matakan da aka dauka daga baya na katse hanyoyin sadarwa ba su ba da wani sakamako mai gamsarwa ba. Don haka lokaci ya yi da za’a duba wasu hanyoyi na dabam. Hanyar Dr Ahmad Gumi na daga hanyoyin da suka kamata a gwada. Muna kira da a duba ta.

  Farfesa Umar Muhammad Labdo Malami a sashen koyar da aikin harkokin addinin Musulunci na jami’ar Yusuf Maitama Sule da ke Kano

  Turawa Abokai

  RUBUTA AMSA

  Rubuta ra'ayinka
  Rubuta Sunanka a nan