Sanata Barau Jibrin ya rabawa ƴan Kanywood Motoci 17 da Babura 100

932

Sanata mai wakilatar Arewacin Kano a zauran majalisar dattawan Najeriya, Sanata Barau Ibrahim Jibrin ya rabawa jaruman Kanywood kayayyakin aiki da su ka haɗa da motoci da kyamarorin ɗaukar hoto mai motsi da ta ɗaukar hoto da fitilar da ake amfani da ita wajen ɗaukar hoto da na’ura ƙara sauti da kuma kwamfiyotoci na miliyoyin Naira.

Taron rabon kayayyakin amfanin a masana’antar ta Kanywood, jaruman masana’antar Kanywood 581 suka amfana da rabon arzikin da Sanata Barau Ibrahim Jibrin.

A lokacin taron da ya gudana ƙarƙashin ofishin shugaban matasan jam’iyyar APC shiyyar Arewacin Kano, Isyaku Abubakar Balan, an raba motoci da babura da kuma kujerar Hajji guda daya.

Abubuwan da Sanata Barau Jibrin ɗin ya rabawa ƴan Kanywood ɗin sun haɗa da Motoci Guda 17 da Babura 100 da Komfuta 80 da Kamara 5 da janereto guda 5. Sauran kayayyakin sun haɗa da Kayan Studio 5 da Kayan Light 5 da kuɗin naira 30,000 ga mutum 100 da Naira 20,000 ga Mutum 100 da kuma kujerar Hajji Mutu 1.

an rabawa wasu daga cikin fitattun jaruman Kanywood sababbin motocin hawa guda 17 da kuma babura guda 80.

Jaruman da su ka rabauta da motocin sun haɗa Ali Nuhu da Adam A Zango da Sani Danja da Yakubu Muhammad da Ado Gwanja da jaruma Hajara Usman.Ado Gwaja, Sani Danja, Tijjani Faraga, Mustapha Naburuska, Da dai sauransu.

A lokacin da ya ke jawabi Isyaku Abubakar Balan ya godewa Sanata Barau Jibrin din a bisa ƙoƙarin da ya ke yi na sanya matasa a cikin harkokin siyasarsa da kuma yadda ya ke ƙoƙarin ganin rayuwar matasan inganta ta hanyar ba su tallafi a dukkanin sana’o’in su domin kyautata rayuwarsu.

Da ta ke jawabin godiya akan wannan kaɓakin arziki da Sanatan ya yiwa ƴan Kanywood ɗin, Hajara Usman ta yi godiya ga Sanatan tare kuma da tabbatar masa da goyon bayan mambobin kungiyar masana’antar Kanywood ɗin a harkokin siyasarsa.

Jarumar Kannywood ɗin ta ce al’ummar jihar Kano shaida akan cewa Sanata Barau Jibrin ne zaɓin Kanawa a shekarar 2023, la’akari da yadda ya ke hidimtawa al’umma ba dare ba rana.

Hajara Usman ta ce za su cigaba da jajircewa wajen ganin burin Sanata Barau ɗin ya cika na zama gwamnan jihar Kano a shekarar 2023.

Taron dai da ya gudana a dakin taro na Meenah da ke birnin Kano, ya samu halarcin shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Alhaji Ahmadu Haruna Zago da tsohon mataimakin gwamnan Kano, Farfesa Hafiz Abubakar da Murtala Alhassan Zainawa da sauran jiga-jigan jam’iyyar APC.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan