Wata tsohuwar Kilaki ta yi ritaya bayan ta kwanta da ‘Maza’ rabin miliyan

811

Beatrice Thompson, wata tsohuwar karuwa Ba’amurkiya ƴar shekara 76 ta bayyana yadda ta kwanta da maza 500,000 da suka haɗa da shugabannin Amurka huɗu a cikin shekara 54.

Thompson, wadda aka yi mata laƙabi da “3$” saboda farashin da take caja a duk kwanciya ɗaya, ta ce ta so ta daina karuwanci tun shekaru da yawa da suka gabata, amma abin da ya hana ta shi ne son cika burinta na kwanciya da maza rabin miliyan.

Beatrice Thompson

“A lokacin da nake ƙarama, ina kwanciya da maza 50 zuwa 100 a duk rana. Na yanke shawarar cewa ba zan daina karuwanci ba sai na kwanta da maza rabin miliyan, amma sai tauraruwata da disashe, saboda haka na daɗe kafin in samu haka”, in ji ta.

Wasu rahotanni sun ce Ƙungiyar Karuwai ta Nevada ta sa wa wannan mata suna “Karuwar Shekara” har sau 17 tsakanin shekarar 1969 da 1992, kuma ta girmama ta da lambar yabo a 2011 bisa gudunmawar da ta bayar a sana’ar karuwanci.

Ta ƙara da cewa tana son tuntuɓar Kundin Tarihi na Duniya wato, Guinness World Records don samun kyauta da kuma taskace irin nasarar da ta samu.

A cewar wannan tsohuwar karuwa, tana da ɗimbin takardu da za su tabbatar da iƙirarinta na kwanciya da maza fiye da rabin miliyan.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan