Ɗalibai Sun Samu Gagarumar Nasara A Jarrabawarmu Ta 2021— WAEC

333

Hukumar Shirya Jarrabawar Kammala Babbar Sakandare ta Afirka ta Yamma, WAEC, ta fitar da sakamakon Jarrabawar Kammala Babbar Sakandare ta Afirka ta Yamma, WASSCE ta 2021.

Shugaban WAEC na Najeriya, Patrick Areghan ne ya bayyana haka ranar Litinin a Legas.

Mista Areghan ya kuma bayyana cewa WAEC ta ƙara kuɗin jarrabawar da ɗalibai ‘yan aji uku suke yi a Mayu/Yuni, da kuma wanda ɗaliban waje suke yi daga N13,950 zuwa N18,000.

A cewarsa, wannan ƙari ya biyo bayan ƙarin kuɗaɗen gudanar da jarrabawar da COVID-19 ta haifar da kuma hauhawar farashi a Najeriya.

Mista Areghan ya ƙara da cewa wannan ƙari zai fara aiki ne da ɗaliban da suke aji uku a yanzu haka.

Da yake bayar da bayani game da sakamakon jarrabawar ta 2021, Mista Areghan ya ce jimillar ɗalibai 1,560,261 ne suka yi jarrabawar, inda 1,274,784 (kaso 87.1) suka samu nasara a aƙalla darussa biyar da suka haɗa da Turanci da Lissafi.

Ya ce wannan nasara ita ce irinta ta farko da ɗalibai suka samu a ‘yan shekarun nan.

Ya ce WAEC ta riƙe sakamakon ɗalibai 170,146 (kaso 10.9) sakamakon samun su da maguɗin jarrabawa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan