Kano Jallabar Hausa: Gidan rediyo na 23 na daf da fara yaɗa shirye-shiryen sa a Kano

298

Shafin gidan rediyon Premier da ke facebook ya bayar da sanarwar cewa nan dan lokaci za su fara yaɗa shirye-shirye sa a jihar Kano.

Sanarwar wacce aka fitar da ita a yammacin yau Talata, inda masu bibiyar su yi fatan alkhairi tare da sambarka bisa wannan lamari.

Yayin da shirye shirye suka yi nisa, ana daf da fara jin amonmu. Daga Gida Mai Lamba 5, Titin Race Course, Nassarawa GRA, Kano” In ji Sanarwar

Sama da shekaru 110 da fara amfani da kafar rediyo a duniya domin isar da sako na fadakarwa ko nishadantar da al’umma. Haka kuma rediyo, hanya ce mai sauki ta saduwa da jama’ar da ke zaune a yankuna masu nisa.

Rediyo dai kafar yaɗa labarai ce mafi girma da aka fi amfani da ita saboda yadda ta ke saurin kai wa ga jama’a masu yawa da kuma sauya tunanin su kan abubuwan da ke faruwa da kuma ba su damar bayyana ra’ayoyin su tare da zabin abin da su ke so.

Katangar Gidan Rediyon Premier da ke birnin Kano


Haka kuma gidajen rediyon kafafe ne da ke bayar da dama ga jama’a domin sanar da su irin wainar da ake toyawa a duniya ta kowanne fanni na rayuwar ɗan Adam.

Akwai gidan rediyo a birnin Kano fiye da guda ashirin (20) kuma a cikin wannan adadi idan ka cire gidan rediyon Bello Dandago da ke kan zangon AM da kuma FM da gidan rediyon ARTV da na Pyramid FM Madobi da kuma na jami’ar Bayero da su ke mallakin gwamnatin jihar Kano da kuma gwamnatin tarayya, duk sauran na ƴan kasuwa ne da su ka kafa domin su mayar da Taro zuwa Sisi.

Ga jerin gidajen rediyo masu zaman kan su da ke jihar Kano kamar haka:

1 – Dala FM

2 – Radio Kano AM/FM

3 – Express Radio

4 – SoundCity Radio

5 – Liberty Radio

6 – Vision FM

7 – Arewa Radio

8 -Guarantee Radio

9 -Wazobia

10 -Cool FM

11 -Rahma Radio

12 -Nasara Radio

13 -BUK FM

14 – Freedom Radio

15 – Hikima Radio (Wasu Dalilai da ake zargin su na da nasaba da siyasa ya sanya ba ta fara aiki ba)

16 – Correct FM

17- ARTV FM

18 – Pyramid FM

19- Aminci Radio

20 -Ray Power FM

21 -Manoma Radio

22 – Jalla Radio FM

23 -Premier Radio FM

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan