Shin Da Gaske Ne Ganduje Zai Tumɓuke Shekarau Daga Sarautar Sardaunan Kano?

298

Gwamnatin Jihar Kano ta musanta jita-jitar da ake yaɗawa cewa tana shirin tumɓuke Malam Ibrahim Shekarau daga Sarautar Sardaunan Kano.

Dangantaka ta yi tsami tsakanin ɓangaren Gwamna Ganduje da na Malam Shekarau tun lokacin da ake shirye-shiryen zaɓen Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kano, inda kowane ɓangare ya zaɓi nasa shugaban.

Ɓangaren Gwamna Ganduje ya zaɓi Abdullahi Abbas a matsayin Shugaban APC na Kano, ɓangaren Shekarau kuma ya zaɓi Haruna Danzago a matsayin shugaba.

Idan dai za a iya tunawa, marigayi Sarki Ado Bayero ne ya naɗa Shekarau Sarautar Sardaunan Kano a 2007.

‘Yan siyasa suna ta yamaɗiɗi cewa Gwamna Ganduje na ƙulle-ƙullen tsige Shekarau daga wannan sarauta sakamakon ƙin yi masa biyayya, inda zai danganta haka da Masarautar Kano.

Da yake mayar da martani game da wannan jita-jita ranar Talata, Mashawarci na Musamman Ga Gwamna Ganduje Kan Harkokin Masarautu, Tijjani Mailafiya Sanka, ya ce wannan labari ne mara tushe ballantana makama.

“Gwamna Ganduje mutum ne mai karamci, mai daɗin mu’amala wanda yake saka mummuna da kyakkyawa, kamar dai yadda ya yi wa Shekarau, lokacin da ya ciro shi daga ɓacewa irin tasiyasa zuwa Majalisar Dattijai, in ji Tijjani.

“E, Ganduje ya yi haka ne da zuciya ɗaya duk da cewa Shekarau ya yi ta adawa da shi tun daga 2003 zuwa 2015, amma a matsayin Gwamna na wanda ba ya riƙe kowa a rai ya ba shi damar zuwa Majalisar Dattijai.

“Ina ruwan Gwamna Ganduje da muƙamin Shekarau na Sardauna? A matsayin Gwamna, zai hau muƙamin Shekarau ne idan aka cire shi? A’a. Ina jin wannan labarin tsagin Shekarau ne suka kitsa shi saboda irin laifukan da suka yi wa Gwamna Ganduje”, ya ƙara da cewa.

Ya ci gaba da cewa: “Duka wannan turka-turka ta samo asali ne daga zaɓen APC wanda tuni uwar jam’iyya ta amince da ɓangaren Ganduje”.

Ya ce hakan ne ya sa Shekarun da magoya bayansa suke ta ƙulla labarai marasa daɗi akan Gwamna.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan