Yadda gwamnatin Ganduje ta ‘jefa’ ɗaliban da su ka rubuta jarabawar NBAIS cikin halin rashin tabbas

358

Wasu ɗalibai a jihar Kano sun ce sun faɗa cikin rashin tabbas game da makomarsu sakamakon matakin gwamnatin jihar na ƙin biya musu kuɗin jarrabawa.

Ɗaliban, waɗanda suka rubuta jarrabawar karshe ta kammala sakandaren Arabiyya, NBAIS, sun yi zargin cewa hukumomin da ke gudanar da jarrabawar sun ƙi ba su sakamakonsu saboda gwamnatin Kano ba ta biya musu kuɗaɗen jarrabawar ba.

Fiye da ɗaliban Arabiyya sama da dubu 13 da ke jihar ta Kano ne ba su san makomar karatunsu ba sakamakon rashin biyan kuɗin jarrabawar ta su.

Wasu daga cikin ɗaliban sun shaidawa Labarai24 cewa tuntuni ya kamata a ba su sakamakon jarrabawar amma hakan ya gagara saboda gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta ƙi biya musu kuɗin jarrabawar.

“Gaskiya ga shi nan na yi karatu amma ban san makomata ba, na yi JAMB ga shi har shekarar ta wuce JAMB ɗin ta lalace ban san a inda nake ba,” a cewar wani ɗalibi da ke son yin karatun lauya amma bai samu sakamakon jarrabawarsa ba.

Kazalika wata ɗaliba da ta rubuta jarabawar ta NBAIS a Kano ta koka akan yadda gwamnatin jihar Kano ta gaza biya musu kuɗin jarrabawar, wanda hakan ya jefa su cikin halin rashin tabbas.

“Mun yi jarrabawar NBAIS tun a cikin shekarar 2018 kuma ga shi sakamakonta har yanzu bai fito ba. Mun je mun tuntuɓi malaman makaranta sun ce ba huruminsu ba ne na gwamnati ne.”

Wata majiya da ta buƙaci a sakaye sunanta ta shaidawa Labarai24 cewa tun daga shekarar 2018 da gwamnatin jihar Kano ta biya rabin kuɗin jarrabawar inda wasu daga cikin ɗaliban su ka samu damar samun sakamakon jarrabawar ta su har yanzu ba ta sake biya ba.

Majiyar ta ce wannan mataki da gwamnatin Kanon ta ɗauka ya haifar da koma baya a ɓangaren Ilimi domin ɗaliban sun gaza cigaba da karatu su.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje

Sai dai ma’aikatar Ilimi ta Kano ta ce ta damu da halin da ɗaliban ke ciki, tana mai ƙarawa da cewa tana tattauna wa da hukumomin jarrabawar NBAIS domin yin sulhu ta yadda za su fitar da sakamakon jarrabawar ɗaliban.

Wannan batu na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin ta ciyo bashin kusan naira biliyan tara ta ke aikin gina gada mai hawa uku, saboda a cewarta yin hakan zai rage cinkoson da ake yawan samu a hanyar.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan