Zargin wawure kuɗin Haraji ya sanya shugaban ƙaramar hukumar Fagge zai gurfana a gaban kuliya

108

Hukumar yaƙi da Cin-hanci mai zaman kanta, ICPC ta maka Shugaban Ƙaramar Hukumar Fagge da ke Jihar Kano, Ibrahim Shehi a gaban babbar kotun jiha.

Tun da farko hukumar ta ICPC na tuhumar Ibrahim Shehi ne da laifuka 4 da su ka shafi zargin sama-da-faɗi da kuɗaɗen harajin ƙaramar hukumar ta Fagge.

Lokacin da ICPC ɗin ta kai ƙarar Shehi, sai a ka tura su kotu mai lamba 16 da ke titin Miller a unguwar bamfai cikin birnin Kano.

A yau Laraba ne dai za a gurfanar da shugaban ƙaramar hukumar da misalin karfe 9 na safe.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan