Ƙirƙirarren Talauci Ne Ya Jefa Arewa Halin Da Ta Ke Ciki— Nasir Salisu Zango

382

Fitaccen ɗan jaridar nan da ke jihar Kano, Nasir Salisu Zango, ya ce sakacin shugabanni ne ya jefa Arewa cikin halin garkuwa da mutane da ta tsinci kanta a ciki.

Zango ya bayyana haka ne a cikin wani rubutu da ya wallafa ranar Alhamis.

Zango ya ce: “Shekarun baya a fim muke ganin ana garkuwa da mutane, daga baya muka fara jin abin a yankin Kudancin Najeriya, sannu a hankali ya shigo Arewa.

“A baya matsalar kamar wasa-wasa amma ta sami gindin zama ta yi zaman ta a yankinmu. Mene ne matsalar ne?

“A fahimta ta, babbar matsalarmu a Arewa ita ce matsalar ƙirƙirarren talauci da jahicin da shugabanninmu suka wanzar a yankunanmu da kuma rashin shiga maganar ‘yan uwan mu idan aka zalunce su. Yanzu yankin Arewa talaka ba shi da gata sai na Allah, kullum fafutuka yake don neman abin da zai ci, amma shugabanninmu kullum ƙirƙirar tsare-tsare suke da za su ƙara ƙuntata masa”.

Ya ci gaba da cewa: “Yanzu an kai gaɓar da abinci ma ya fara gagarar dubban mutane, duk abin da ka ɗauka za ka iske an bar mu a baya.

“Talauci ya yi mana katutu, amma shugabanninmu da jagororinmu suna rige-rigen hawa motocin miliyan tsababa. Wannan magana ce bayyananniya. Ku duba irin motocin da suke hawa.

“Noma da muke dogara da shi yanzu ya fara gagarar mu. Abin kunya da takaici har yanzu da garma da fartanya ake noma, amma kullum ana maganar cewa an inganta noma an samar da taki”.

“Ilimi kuwa sun bar makarantunmu sun lalace, azuzuwa a jagwalgwale abin ba kyan gani, dama ‘ya’yansu ba a nan suke karatu ba, don haka ba su damu ba ko a jikinsu.

“Haka muke ta rayuwa kowa ya zuba ido, an kasa samar war da yankin mafita.

“Yanzu ga matsalar garkuwa da mutane kowa yana cikin firgici, amma shekara da shekaru an kasa shawo kanta. Wai don Allah mene ne laifinmu ne?

“Mafi yawan shugabanninmu ba sa kishin mu, domin adalcinsu b aya tashi sai wani namu ya yi kuskure. Nnmadi Kanu babban ɗan ta’adda ne wanda ya yi sanadiyyar kisan mutane, amma dattijan yankinsa ƙoƙari suke a sake shi, duk da cin amanar ƙasa da ya yi. Amma Yunusa Yellow, duk girman laifin sa bai kai na Kanu ba, yau an ma daina maganarsa.

“Ba ina nufin Yunusa bai yi laifi ba. Amma ina ga yadda aka tafiyar da maganarsa, ya kamata a ce an yi wani abu a kansa. Wannan dai ra’ayina ne, amma na san ko kusa laifin sa bai kai na Kanu ba.

“Da yawan shugabannin yankinmu sun gaza sun ba mu kunya, kuma sakacinsu ne ya jefa mu cikin wannan hali. Allah ya samar mana da mafita, ya kawar da duk wanda ya hana ruwa gudu wajen ci gaban yankinmu”, ya ƙara da haka.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan