Sai da na kusa rasa raina akan ganin Buhari ya zama shugaban Najeriya – Sanata Hanga

624

Tsohon shugaban jam’iyyar CPC na ƙasa, Sanata Rufa’i Sani Hanga ya bayyana cewa ya kusa rasa ransa akan goyon shugaba Muhammadu Buhari ya zama shugaban Najeriya.

Rufa’i Sani Hanga wanda tsohon ɗan majalisar dattawa ne da ya walilci mazabar Kano ta tsakiya ya ƙara da cewa ya kashe sama da Naira miliyan 100 daga aljihunsa wajen ganin Buharin ya zama shugaban ƙasa, amma sai aka wayi gari shugaba Buharin ya yi watsi da shi da buƙata ta biya.

Tsohon Sanatan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke tattaunawa da manema labarai a Kano, kamar yadda jaridar Blueprint ta rawaito.

Haka kuma ya ce da daman waɗanda suka dafawa Buhari ya samu ɗarewa kujerar shugabancin ƙasa, duk an watsa musu ƙasa a ido. Yana mai cewa, yanzu Buhari ya zaɓi wasu ne daban suke kewaye da shi waɗanda ba su bai wa yaƙin neman zaɓensa gudunmawa ba kuma ba ‘yan jam’iyyarsa ba.

“Na rasa gidajena, ni da iyalaina mun kusa rasa rayukanmu wajen yaƙin neman zaɓen Buhari cikin dare a yankin Arewa ko Kudu, amma bayan da aka rantsar da Buhari sai ya maishe ni tare da galibin waɗanda suka yi masa aiki saniyar ware”, in ji Hanga.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan