A ƙarshe gwamnatin Kaduna za ta dawo da layukan wayar sadarwa

163

Gwamnatin Jihar Kaduna ta baiyana cewa ta tuntuɓi ma’aikatun gwamnatin tarayya domin dawo da layukan wayar sadarwa da a ka katse a wasu ƙananan hukumomi a jihar sakamakon rashin tsaro.

A tuna cewa a watan Oktoba ne dai jami’an tsaro su ka nemi gwamnatin da ta katse layukan wayar domin taimaka musu a yaƙin da su ke da ƴan ta’adda a jihar.

A yau Juma’a kuma sai gwamnatin ta ce jami’an tsaron sun bata shawarar cewa za ta iya dawo da layukan wayar.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar, Samuel Aruwan ne ya baiyana hakan a taron manema labarai a yau.

Aruwan ya baiyana cewa katse layukan wayar da sauran matakan tsaro sun taimakawa jami’an tsaro sun cimma nasarori a kan yaƙi da rashin tsaro a jihar.

“Daɗewa a kan irin wannan matakan kuma yana da nashi naƙasun idan a ka yi duba da rayuwar al’umma da kuma harkar tattalin arziki.

“A na baiwa jama’a shawarar cewa a guraren da katse layukan ya shafa zai faru nan da ƴan kwanaki kaɗan saboda kamfanonin na nan na ƙoƙarin samar da wutar lantarki domin cimma aikin cikin nasara,”

Aruwan ya baiwa jama’ar yankunan da abinda ya shafa haƙuri, in da ya ƙara da cewa gwamnatin jihar na rarrashin al’umma kuma tana yaba mu su a bisa haƙuri da jajircewar da su ka yi a lokacin da a yanke layukan wayar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan