El-Rufa’i Ya Rage Wa Ma’aikatan Kaduna Ranakun Aiki

240

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce daga ranar 1 Disamba, 2021 ma’aikatan jihar za su dinga yin aiki daga Litinin zuwa Alhamis.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Gwamnatin Jihar Kaduna ta fitar ranar Litinin.

A cewar sanarwar, wannan matakin zai bai wa ma’aikatan damar yin aikin kwana ɗaya daga gida, domin inganta aiki da ba su damar samun lokaci ga iyalinsu da kuma samun lokacin noma, kamar yadda BBC Hausa ta rawaito.

Sanarwar ta ce matakin na daga cikin darussan da aka koya lokacin annobar COVID-19 da ke buƙatar samun lokacin samun annashawa saɓanin tsohon tsarin da aka saba da shi na aiki.

Sai dai sanarwar ta ce makarantu da ma’aikatan lafiya za su ci gaba da aiki ne daga Litinin zuwa Juma’a, kamar yadda aka saba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan