Gwamna Ganduje ya ginawa jami’an tsaron farin kaya masallaci a Kano

288

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranci buɗe masallacin da gidauniyar sa ta gina harabar shalkwatar rundunar tsaron farin kaya da ke Kano.

Tun da farko hadimi na musamman ga gwamna Abdullahi Umar Ganduje, akan ɗaukar hoto, Aminu Ibrahim ne ya wallafa hotunan buɗe masallacin da gwamnan ya jagoranta.

Bayan buɗe masallacin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranci sauran waɗanda su ka samu damar halartar buɗe masallacin sallah.

A lokacin buɗe masallacin gwamnan na tare da mataimakin sa Dakta Nasiru Yusuf Gawuna da kuma shugaban ƙungiyar Izala na kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan