Zulum zai Ɗauki Nauyin Karatun Marayu 500 na ‘yan sa-kai d aka Kashe a Yaƙin Boko Haram

176

Gwamnan Borno Babagana Umara Zulum ya sanar da shirin ɗaukar nauyin karatun marayu 500 na ƴan sa-kai da ake kira civilian JTF da ya kira jaruman Borno waɗanda aka kashe a yaƙi da Boko Haram.

Shirin wanda ya ƙunshi kula da matan ‘yaan sa-kan da suka haɗa da ƴan banga da mafarauta da suka mutu a fagen yaƙi da Boko Haram da Iswap.

Zulum ya sanar da matakin ne lokacin da yake gabatar da kasafin kuɗi na shekarar 2022, a cewar Sanarwar da gwamnatin Borno ta fitar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan