Ina Jajanta Wa Kanawa Bisa Haɗarin Kwale-Kwale A Ɓagwai— Buhari

151

Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana baƙin cikinsa bisa haɗarin kwale-kwale da ya afku a ƙaramar hukumar Ɓagwai dake Jihar Kano wanda ya yi sanadiyyar rasuwar fiye da mutum 20.

Shugaba Buhari ya bayyana damuwarsa tasa ne ta hannun Mai Magana da Yawunsa, Garba Shehu, ranar Laraba a Abuja.

Ya tabbatar da cewa hukumomin Gwamnatin Tarayya za su kawo dukkan taimakon da ake buƙata wajen aikin ceto.

“Ana nan ana ci gaba da ƙoƙari wajen ceto fasinjojin da har yanzu ba a gano ba, ina taya dukkan ‘yan Najeriya addu’ar Allah ya ji ƙan waɗanda suka rasu kuma Allah ya tsare saura”, in ji shi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan