Yan bangar siyasa sun bankawa ofishin jam’iyyar APC ɓangaren Shekarau wuta a Kano

137

Wasu matasa sun cinna wa ofishin jam’iyyar APC ɓangaren tsohon gwamna wuta a Kano.

Shaidu sun bayyanawa manema labarai cewar matasan sun fi 100 da suka abka wa ofishin jam’iyyar.

Wannan na zuwa a yayin da wata kotu a Abuja ta rushe shugabancin ɓangaren gwamna Ganduje tare da tabbatar da jagorancin ɓangaren Shekarau.

Rikicin siyasar APC a Kano na ci gaba da ɗaukar hankali a Najeriya tun bayan gudanar da zaɓen shugabannin jam’iyyar ɓangare biyu, inda wasu ke ganin rabuwar kai a Kano wata babbar ɓaraka ce ga APC

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan