Kano: EFCC Ta Cafke ‘Yan Damfara Ta Hanyar ATM

353

Hukumar Hukunta Masu Yi Wa Tattalin Arziƙin Najeriya Ta’annadi, EFCC, ta cafke wasu mutane uku a Jihar Kano ɗauke da da katin cirar kuɗi na ATM har guda 1444.

EFCC ta cafke mutanen ne a Fili Jirgin Saman Ƙasa da Ƙasa na Malam Aminu Kano, Kano.

Hukumar ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da Mai Magana da Yawunta, Wilson Uwujaren, ya fitar ranar Juma’a a Kano.

A cewar EFCC, mutanen suna ƙoƙarin yin simogar katin ATM 1,444 ne zuwa wasu ƙasashen ƙetare.

Ta ce ta yi wannan kamen ne tsakanin 24 ga Nuwamba zuwa 1 ga Disamba, 2021.

A cewar EFCC, mutanen su ne Abdullahi Usman, Musa Abubakar da Abdulwahid Auwalu.

EFCC ta ce ta samu Abdullahi, wanda yake shirin zuwa Dubai, Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, UAE, da katin ATM guda 714.

Hukumar ta ƙara da cewa Abdullahi kuma, wanda yake kan hanyar sa ta zuwa Saudiyya, ta same shi da katin ATM 298.

Abdulwahid kuma, wanda ke shirin tafiya birnin Santambul na Turkiyya, ta same shi da kati 132.

“Za a maka mutanen da ake zargin kotu da zarar an kammala bincike”, in ji Mista Uwujaren.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan