Yau ta ke ranar masu buƙata ta musamman: Wanne hali su ke ciki a Najeriya?

123

Ranar 3 ga watan Disambar kowacce shekara ranar ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware dan bikin ranar mutane masu buƙata ta musamman ta duniya da ake yi shekara shekara.

Tun a shekarar 1976 majalisar ta ayyana 1981 a matsayin shekarar mutane masu bukata ta musamman, inda kuma aka fara bikin ranar daga 3 ga watan Disamba 1992.

Manufar ware ranar ita ce fadakar da al’umma batutuwa da suka shafi nakasa, da k’ok’arin bayyana irin hakkokin da nak’asassu suke da su.

An kuma yi batun alfanun da za a iya samu idan aka shigar da mutanen da ke da ‘ cikin dukkan al’amura na rayuwa da suka had’a da siyasa da tattalin arziki da kuma zamanakewa.

Nakasassu dai suna gamuwa da k’alubale daban-daban a ko’ina a duk fadin duniya.

Wata matsala da tafi damun wannan rukuni na masu bukata ta musamman ita ce yadda wasu daga cikin al’umma ke nuna musu kyara, tsangwama tare da ganin kamar su ba mutane kamar kowa ba.

To sai dai ko shin a arewacin Najeriya wadan nan jama’a suna samun kulawar daga hukumomi ? Kuma ko akwai wani yunkuri da kungiyoyin masu bukata ta musamman din suke yi domin tabbatar da wannan gwagwarmayar tasu, ta kai ga cimma nasara ?

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan