Janar Mohammed Inuwa Wushishi, tsohon hafsan sojojin Najeriya ya rasu

273

Wasu rahotanni sun bayyana cewa Allah ya yiwa tsohon babban hafsan sojojin Najeriya, Janar Muhammad Inuwa Wushishi rasuwa yana da shekaru 81 da haihuwa.

Janar Inuwa Wushishi ya taɓa riƙe muƙamin babban hafsan sojojin ƙasa a lokacin jamhuriya ta biyu.

Marigayin ya rasu a wani asibiti da ke birnin London bayan ya yi fama da jinya kamar yadda wata majiya daga iyalin mamacin ta tabbatarwa da Labarai24.

Kuma bayan ya yi ritaya Janar Wushishi ya koma kasuwanci, inda har ma ya rike shugabancin majalisar zartarwa ta kamfanin UAC a Najeriya da kuma darakta a bankin Stanbic IBTC.

Marigayin ya bar mata daya da ‘ya’ya bakwai, ciki har da tsohon kwamishinan kasuwanci a jihar Naija Kabiru Muhammadu Wushishi.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan