Matsalar Tsaro: Ƴan bindiga sun yi awon gaba da gwamman mutane a Kaduna

312

Rundunar ƴan sandan Jihar Kaduna ta bayyana cewa ƴan bindiga sun yi garkuwa da mutum sama da 20 a unguwar Gimbiya dake Sabon Tasha, da ke yankin Ƙaramar Hukumar Chikun.

Kakakin rundunar ƴan sanda ta jihar, Mohammed Jalige, wanda ya sanar da haka ranar Juma’a a gidan talabijin na ChannelsTV ya ce ƴan bindigan sun farwa unguwar Gimbiya da misalin ƙarfe 1:00 na dare, lokacin da mutane ke kwance suna barci.

Jalige ya ce ƴan bindigan sun shiga unguwar ɗauke da manyan makamai, inda su ka yi kan-mai-uwa-da-wabi, inda a dalilin hakan, mutum biyu su ka rasu.

Ya ce rundunar ta fantsama farautar maharan domin ceto waɗanda a ka yi garkuwa da su.

Wani mazaunin unguwar, Gyara Guga ya tabbatar wa da jaridar PREMIUM TIMES da wannan hari, sai dai ya ce ba zai iya tabbatar da adadin yawan mutanen da maharan su ka sace ba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan