Shugaba Emmanuel Macron ya kai ziyara ƙasar Saudiyya

142

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya isa ƙasar Saudiyya inda yake tattaunawa da yariman ƙasar.

Wannan ne karo na farko da Mohammed bin Salman yake irin wannan tattaunawar da wani babban shugaba daga ƙasashen yamma tun bayan da aka kashe ɗan jarida Jamal Khashoggi.

Mista Macron da kuma yarima bin Salman sun gaisa da juna a lokacin da suka soma tattaunawa a Jeddah.

Mista Macron ya mayar da martani kan ƙorafin da wasu ƙungiyoyin kare haƙƙin bil adama suke yi inda ya ce ziyarar da ya kai ba tana nufin ya manta da kisan da aka yi shekara uku da ta gabata ba na Khashoggi.

Shugabar ƙungiyar Amnesty International Agnes Callamard, ta zargi Mista Macron da zubar da darajar ƙansa da ƙasarsa.

Tuni dai dama Saudiya ta musanta cewa ita ta bayar da umarnin kisan Mista Khashoggi a ƙasar Turkiyya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan