Gwamnatin Kano ta rufe wasu gidajen man fetur saboda zargin Ha’inci

436

Hukumar kare hakkin masu sayen kayan masarufi ta jihar Kano (KSCPC) ta rufe wasu gidajen sayar da man fetur sakamakon kama su da ha’intar abokan cinikayya ta hanyar rage lita.

Shugaban hukumar ta KSCPC, Janar Idris Bello Dambazau mai ritaya ne ya sanar da haka a shafinsa na facebook a jiya Asabar.

Jami’an hukumar KSCPC a lokacin da su ke aikin rufe gidajen man

Idris Bello Dambazau ya ce sun ɗauki matakin rufe gidajen man ne sakamakon samun su da rage lita wanda hakan ya saɓa da doka.

Gidan man fetur na NNPC

Jami’an Hukumar KSCPC sun rufe wasu gidajen sayar da mai fetur domin suna rage hannu a lita (litre) a yau Asabar 4 ga Disamba 2021″.

SID Oil and Gas

Gidajen sayar da man da aka garƙame sakamakon rage lita sun haɗa da A.Y.M Shafa da Matrix Energy da Kabiru Isa Oli and Gas, da SID Oil and Gas da Fara Fara Oil and Gas da NNPC da kuma Oando.

Gidan man fetur na A.Y. M Shafa da aka garƙame

Ƴan Najeriya dai sun daɗe suna zargin gidajen sayar da man da aikata Ha’inci ta hanyar rage litar man fetur wanda hakan ke cutar da jama’a.

Gidan man fetur na Matrix Energy
Fara Fara Oil and Gas
Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan