Jami’an DSS sun kama Janar Idris Bello Dambazau a Kano

525

Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya, wato DSS, a jihar Kano sun kama shugaban hukumar kare hakkin masu siyan kaya ta jihar Kano, Janar Idris Bello Dambazau, bisa zarginsa da yiwa tattalin arziki kafar ungulu.

Tun da farko hukumar da Idris Bello Dambazau ke shugabanta wato KSCPC ce ta garƙame wasu gidajen sayar da man fetur guda 7 a jihar Kano.

Sai dai jami’an tsaron na DSS sun bayyana cewa Dambazau din bai bi matakan da doka ta tanada wajen rufe gidajen man ba.

Haka kuma duk ƙoƙarin da aka yi wajen ganin Dambazau ya bude gidajen man da ya rufe amma abin ya ci tura.

Wanna ce ta sanya jami’an hukumar tsaron farin kayan su ka cafke shi tare da zargin yunƙurin haifar da karancin mai a jihar Kano, bayan kuma babu karancinsa, kuma yin hakan ya saba da sashi na 48 cikin kundin tsarin mulkin Nigeria, kamar yadda wata majiya daga hukumar ta shaida.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan