Na Ga Ayar Da Ta Yi Umarnin Miji Ya Daki Matarsa A Cikin Ƙur’ani— Naziru Sarkin Waƙa

503

Fitaccen mawakin nan ɗan asalin jihar Kano, Nazir M. Ahmad, da aka fi sani da Sarkin Waƙa, ya yi wata wallafa a shafin sada zumunta na Instagram game da batun dukan mata— a Musulunci—wallafar da ta tayar da ƙura a tsakanin mabiyansa.

Tun da farko dai Sarkin Waƙa ya wallafa hoton shafin Ƙur’ani Mai Girma a cikin Suratun Nisa’i mai ɗauke da ayar da ta yi bayani game da dukan mata idan dukkan matakan ladabtarwa sun ƙi yin aiki.

Bayan nan ne sai mabiyansa suka fara mayar da martani kala-kala.

Sarkin Waƙa ya ce ya yi wannan wallafar ne saboda wadanda suka ce Ƙur’ani ya ce kar a daki mata.

“Ni dai na ga ayar da ta ce mutum ya daki matarsa idan ta ci tura, sai dai a taya ni nemo wadda ta ce kar a daki mata. Na gode”.

Ga irin yadda mutane suka mayar da martani game da wannan wallafa ta Sarkin Waƙa.

Wani sashi na martanin mabiyan Sarkin Waƙa

Daga baya kuma Sarkin Waƙa ya wallafa wani bidiyo a shafin nasa na Instagram, inda ya yi cikakken martani ga masu caccakar sa.

A cikin bidiyon, ya yi kira ga jama’a da su nemi ilimin addini, kuma su riƙa tuntuɓar malamai kafin su yi magana akan duk wani abu da ya shafi addini.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan