Sarkin Kano Aminu Ado Bayero na shirin Angwancewa da tsohuwar budurwarsa

1851

Wasu rahotanni da jaridar Daily Nigerian ta wallafa ya bayyana cewa mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero na daf da angwancewa da tsohuwar budurwarsa mai suna Hajiyayye.

Aminu Ado Bayero zai auri Hajiyayye ne da ke unguwar Dorayi a yankin ƙaramar hukumar Gwale, bayan ya shafe tsahon shekaru da matarsa guda ɗaya da ya’yansa guda huɗu.

Wata majiya ta bayyana cewa tuni shirye-shirye su ka yi nisa tsakanin waliyan mai martaba Sarki da na Amarya Hajiyayye.

Amarya Hajiyayye Dorayi

Haka kuma majiyar ta ce za a yi bikin auren ne cikin sirri ba tare da an yi wani babban taro ba, la’akari da cewa iyayen amaryar ba wasu fitattun mutane ba ne.

Majiyar ta ƙara da cewa an yi nufin ɗaura auren a cikin ƴan kwanaki. Sai dai an dinga daga ranar auren ne tun da ba a buƙatar taron jama’a, amma daga yanzu zuwa kowanne lokaci za a daura auren.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan