Ɗalibai Su Tabbatar Suna Da NIN Kafin Su Yi Rijistar UTME— JAMB

223

Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Manyan Makarantun Gaba da Sakandare, JAMB, ta buƙaci ɗalibai da za su zana Jarabawar Shiga Manyan Makarantun Gaba da Sakandare, UTME, ta 2022 da su tabbatar sun mallaki Lambar Shaidar Zama Ɗan Ƙasa, NIN, kafin jarrabawar.

Magatakardar Hukumar, ne ya bayyana haka ne ranar Litinin a Abuja.

JAMB ta ce kwanan nan za ta fara siyar da fom na jarrabawar UTME ta 2022.

“A yanzu hukumar, tana tattaunawa da manyan abokan aikinta wajen bada horo don tabbatar da cewa matsala da zarar an fara siyar da famafaman.

“Fitar da wannan sanarwa ya yi daidai da ƙudirin hukumar na tabbatar da cewa ɗalibai da suke son yin jarrabawar sun shirya yadda ya kamata”, in ji JAMB.

“Haka kuma, ana sa ran wannan sanarwa za ta zama zaburarwa ga wanda yake son yin rijista su tabbatar da cewa da farko sun samu NIN, wanda shi ne babban abin buƙata kafin a yi rijistar UTME.

“Ga waɗanda suke son siyan kowane daga cikin takardun yin rijista, ana shawarartar su da farko su samu NIN kuma su sabar wa kansu da manhajar JAMB mai suna Integrated Brochure and Syllabus System, IBASS.

“Zai ba su haske game da irin kwasa-kwasan da ake buƙata su karanta kafin zana jarabawa”, ta ƙara da haka.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan