Wani matashi a Kano ya buƙaci a bashi dama su kece raini da Sheikh Abduljabbar Kabara

433

Wani matashi a jihar Kano da ke arewacin Najeriya, Muhammad Bashir ya buƙaci mahukunta a jihar da su ba shi dama ya kece raini tsakaninsa da fitaccen Malamin addinin Islama nan, Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ta hanyar yin kokawa.

Muhammad Bashir wanda ɗan jarida ne kuma mai yin sharhi akan al’amuran yau da kullum ne ya bayyana hakan a cikin wasu takardu da aikewa da hukumar ƴan sanda da hukumar Hisba da kuma kwamishinan harkokin addinai da su ke jihar Kano.

A cikin takardar Bashir ya buƙaci wadannan hukumomi da su amince masa tare da kai su filin kofar fadar mai martaba Sarkin Kano, domin su raba raini tsaknainsa da Abduljabbar Kabara.

“Ina son hukuma ta sahale mani yin fito na fito, ba tare da makami ba, da Abduljabbar Kabara a filin gidan Sarkin Kano, Kofar Kudu – abin da ake kira da Mubaraza wanda tana da asali a addini, idan ba cutarwa a addini”.

“Wannan Mubaraza ina son a yi ta ne kawai domin nunawa Sheikh Abduljabbar da mabiyansa cewa al’ummar jihar Kano, waɗanda ba mabiyansa ba, mun fi shi gaskiya a hujjoji da kuma ƙarfin damtse. Kuma ba kisa ko rauni za a jiwa wani ba, sai dai kaye kawai”.

Wasu Malaman jihar Kano sun soki wa’azin malamin da yin kalamai na ɓatanci ga Annabi SAW, inda suka kai kukansu ga gwamnati.

Idan za a iya tunawa dai a cikin watan Yulin shekarar nan ne gwamnatin jihar Kano ta shirya wata mukabala tsakanin Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara da Malaman da su ke ƙalubalantar irin karatun da ya ke yi.

Haka kuma Gwamnatin Kano ta ce manufar muƙabalar shi ne tabbatar da gaskiya da inganci bisa dacewa kan abin da malam Abduljabbar ya ke bayyanawa ga Annabi Muhammad SAW, a rubuce-rubucensa, wanda kuma za a bayar da hujja akan Ayoyin Kur’ani da hadisai.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan