Malamin makaranta ya yiwa ɗalibarsa mai fama da taɓin hankali fyaɗe a Kano

770

A yau Alhamis wata kotun majistire da ke jihar Kano, ta bayar da umarnin aikewa da wani Malamin makaranta mai suna Sukairaj Kabir zuwa gidan gyaran hali sakamakon samunsa da aikata laifin fyaɗe ga wata ɗalibarsa ƴar kimanin shekara 15 da ta ke fama da taɓin hankali.

Malam Sukairaj Kabir wanda mazaunin unguwar Rimin Auzunawa ne da ke birnin Kano, ya yaudari ɗalibar ta sa ce wacce ta ke fama da larurar taɓin hankali a tsakanin shekarun 2018 da 2021 a unguwar Tudun Yola da ke yankin ƙaramar hukumar Gwale, kamar yadda lauya mai gabatar da ƙara ta shaidawa kotu.

Tun da farko lauya mai gabatar da ƙara Asma’u Ado ta bayyanawa kotun cewa wanda ake zargin da aikata laifin ya yaudari ɗalibar ta sa ne inda ya kai ta wani ajin islamiyya da ke unguwar Tudun Yola tare da yi mata fyaɗe.

Haka kuma Barista Asma’u ta ce wannan malamin makaranta ya fara lalata da ɗalibar ne tun tana shekaru 12 a duniya.

Ta ƙara da cewa hakan kuma ya saba da sashe na 238 da kuma sashe na 283 na kundin Penal Code.

A ƙarshe mai shari’a Mustapha Sa’ad Datti ya bayar da umarnin a cigaba da tsare Sukairaj Kabir a gidan gyaran hali har zuwa rana 10 ga watan Janairun shekarar 2022.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan