An yi bikin naɗin Fatima Aliyu Barau a matsayin Fulanin Dambo a masarautar Ingawa

3447

A yau Lahadi, mai girma Sarkin Fulanin Dambo Hakimin Ingawa da ke jihar Katsina a arewacin Najeriya, Alhaji Tukur Suleiman Dambo II ya naɗa Hajiya Fatima Aliyu Barau CIISM a matsayin Fulanin Ingawa.

Fatima Aliyu Barau ta fito ne daga Zuri’ar Sarkin Fulani Dambo Tukur, shi kuma Dambo Tukur shi ne Dambo na hudu kafin zuwa ga Dambo na yanzu maici, wanda kaka ne gareshi.

Taron naɗin sarautar ya gudana ne a fadar Mai girma Hakimin Ingawa Sarkin Fulani Dambo dake garin Ingawa cikin karamar hukumar Ingawa.

Fulanin Ingawa, Hajiya Fatima Aliyu Barau CIISM

Fulanin Dambo dai ta kasance ƴar asalin jihar Katsina, haifaffiyar garin Kaduna da ke Arewacin Najeriya, ita ta kafa gidauniyar Kaltufat wato Kaltufat Foundation da ke taimakon marayu da masu ƙaramin ƙarfi a duk inda aka buƙaci taimakonta kuma ta ke da sararin taimakawa.

Fulanin Ingawa

Taron bikin naɗin sarautar dai ya samu halartar ɗimbin al’umma daga ciki da wajen jihar Katsina.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan