Buɗaɗɗiyar wasika zuwa ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Sanata Rabi’u Kwankwaso

  2835

  “An wallafa wannan wasikar ne a ranar 24 ga watan Maris na shekarar 2016, lokacin da rikicin siyasa tsakanin tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ke ƙamari, sai dai kuma kamar yadda masu iya magana kan ce ‘Ajiya Maganin Wata Rana’, wannan haka ya ke domin a halin da ake ciki yanzu sakon da ke cikin wannan wasikar ya na da matuƙar muhimmanci ga bangarorin guda biyu.”

  Bayan gaisuwa,

  Na rubuta wannan wasikar ne domin bayyana matukar damuwata gare ku dangane da sabanin da ya afku tsakaninku, a matsayinku na jagororin siyasar jihar Kano, musamman idan aka lura da tsawon shekarun da kuka kwashe kuna mu’amalar siyasa a matsayin aminin juna.

  Alal hakika duk wadanda ke kokarin rura wutar gaba a tsakaninku tare da kawo karshen amincinku mai yawan tarihi cikin kasa da shekara guda, ba masoyanku bane, sai dai ‘yan jagaliyar siyasa wadanda ke sa ran samun “kayan aiki” sakamakon wannan rikici.

  Idan baku manta ba, na yi ta zarya tsakanin gidajenku a asirce domin kokarin tabbatar da sulhu tsakaninku.


  Ban taba yin kasa a gwiwa ba, tun daga  somi-somin sabanin, zuwa lokacin da aka fara cacar-baki har yanzu kuma da rikicin ya bayyana a fili. Na dauki lokaci kafin rubuta muku wannan budaddiyar wasikar ne saboda nauyin tabbatar da amincewa da kudirin kasafin kudi da aka dora wa kwamitin da nake shugabanta a majalisar wakilai. Ba shakka kun isa shaidu na irin kokarin da na yi tayi na sasantaku duk da wannan nauyin dake kai na.

  Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Dakta Abdulmumin Jibrin Kofa

  Hakika ni ba zan iya munafarta daya daga cikinku ba. Don haka nake ganin babbar kauna, da biyayyar da ya kamata in nuna muku, ita ce in nemi hanyar sasantaku domin kada ‘yan-bani-na-iya su jawo zubewar mutuncin da kuka jima kuna da shi cikin al’umma.

  Ina nan akan bakata, cewa daukar layi a cikin wannan rikici itace babbar hanyar da zata kara rura wutarsa, kuma ba za ta zamo alheri gareku ba, ko ga jam’iyyarmu ko kuma dimbin magoya bayanmu ba.


  Ranku ya dade, na tabbatar kuna sane da cewa ni ban taba rattaba hannu kan wata takarda dake nuna goyon baya ga kowanne bangare ba, a kokarin da nake yi na sasanta tsakaninku – rawar da nake ganin ita tafi dacewa ga dukkan ‘yan majalisa da sauran shuwagabanni su taka.
  A ranar Laraba, ina zauren majalisa ina shirya takardun kasafin kudin bana, abokin aikina, Aliyu Madaki ya nemi in sa hannu kan wani rubutu mai sakin layi uku. Nan take na rattaba hannu don na ga batun ya dace da ra’ayina na neman sulhu ba tare da nuna goyon baya ga wani bangare ba.


  Idan har an sauya maganar da ke kan takardar domin ta nuna goyon baya ga wani bangare to ni dai ina nan kan bakata na cewa bani da bangare sai dai kokarin sulhunta rikicin.

  Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da Dakta Abdulmumin Jibrin Kofa

  Duk da tarin biyayyar da nake yi wa sanata Kwankwaso, wanda ya raine ni a siyasance har na kai matsayin da nake a yau, ni ba zan shiga cikin jerin masu yi wa gwamna Ganduje rashin kunya ba, ganin yadda yake kimanta ni.

  Ya ku masu girma shugabannina, hakika ina girmamaku duk ku biyun, kuma ina da kyakkyawar alaka da kowannenku.


  Afkuwar wannan rikici abin takaici ne a lokacin da kuka kai kololuwa a gwagwarmayarku ta siyasa, kuma ku ke kokarin horar da halifofinku a siyasance. Abin da yafi tayar min da hankali kuma, shi ne ganin mabiyanku, wadanda ke zaman lumana da juna a watanni baya, yanzu sun zama abokan gaba suna ta aikin rushe ginin da kuka yi mana.

  Bugu da kari, ina fargabar tasirin da wannan rikicin zai yi idan ya yadu zuwa wasu jihohin, kasancewar Kano ita ce cibiyar siyasar arewacin Nigeria. Wannan na daga cikin manyan dalilan da nake ganin ya wajaba duk manyan kwarai su shiga cikin kokarin sulhunta tsakaninku. Hausawa na cewa “Idan gemun dan uwanka ya kama da wuta, shafawa naka ruwa.”

  A yayinda nake jinjinawa shugaban kasa, da jam’iyyarmu, da gwamnoni bakwai na jihohin arewa maso yammacin Nigeria, da sarkin Kano, da sauran fitattun mutane da suke kokarin sasanta wannan rikici, ina kuma kira ga ‘yan uwana ‘yan majalisa da suma su yi koyi da su.

  Bayan da nayi nazari mai zurfi akan wannan rikici, na tabbatar da cewa babu daya daga cikinku da rigimar zata amfanar. Jam’iyya zata ji jiki. Hankulanku za su rabu. Sannan sharrin abun zai kare kan talakawa. Su kuma abokan hamayyarmu na siyasa wadanda mu ka kayar a baya, zasu yi amfani da damar wurin sake gina kansu. Domin kuwa sai bango ya tsage kadangare ke samun wurin shiga.

  A bayyane take cewa rikicin nan ya sha kanku domin magoya bayan bangarorin biyu sun karbe ragamar rikicin, abinda ke rage muku ikon sasanta fitinar.


  Idan har ana son samar da sulhu na gaskiya, ya kamata ku shigo da manyan magoya bayanku wadanda sune suka haddasa rigimar, kuma suke kara iza wutarsa, domin su san yadda zasu yayyafa ruwan kashe ta.

  Ya ku shuwagabannina na kwarai, bayan duk tarbiyyar alherin da kuka bamu, mu ‘ya’yanku na siyasa, wane irin gado ku ke so ku bar mana? Tabbas bai kamata ku bar mana gadon rigima ba, da rusa ginin da kuka assasa.

  A yayinda nake fatan ganin an samu ingantaccen sulhu a tsakaninku, ina kara jaddda matsayina na kokarin yin duk mai yiwuwa na ganin an sasantaku.

  Bissalam,
  Abdulmumini Jibrin, PhD

  Cc:   Shugaban kasa Muahammadu Buhari

  Shugaban jam’iyyar APC na kasa,
  Chief John Odigie-Oyegun,

  Shugaban majalisar gwamnoni
  Mai martaba sarkin Kano

  Turawa Abokai

  RUBUTA AMSA

  Rubuta ra'ayinka
  Rubuta Sunanka a nan