Katsina A Hannun Ƴan Bindiga: Duk wanda ya mutu wajen kare ransa yayi Shahada – Masari

253

Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari, ya sake yin kira ga al’ummar jiharsa da su tashi tsaye domin baiwa kansu kariya da kuma tunkarar barazanar ‘yan bindiga da ke cigaba da kisan jama’a, cin zarafi da kuma yin garkuwa da mutane babu kakkautawa.

Masari ya bayyana haka ne, a yayin wata ganawa da manema labarai a garin Katsina, inda ya koka kan cewar yayi kiran ne la’akari da cewar, Jihar tasa ba ta da isasshen adadin jami’an tsaron da za su murkushe ‘yan bindigar da ta’addancinsu ke karuwa a sassan Katsina, musamman a yankunan karkara.

Gwamnan na Katsina wanda ya bayyana mamaki akan yadda gungun miyagu ke mallakar makamai, ba tare da mutanen kirki sun mallaki nasu ba, ya karfafawa mutane gwiwa da cewar, kare kai, ko iyali na da asali a addinin Musulunci, ta yadda duk wanda ya rasa ransa yayin hakan ana sa ran ya samu gwaggwaban lada na yin Shahada.

Wakilinmu da ya samu halartar taron manema labaran, ya ruwaito mana cewar, gwamnan na Katsina ya sha alwashin taimakawa mutanen da suka shirya daukar matakan kare kansu daga ta’addancin ‘yan bindiga.

Gwamnan Jihar Katsina Amuni Bello Masari kan matsalar hare-haren yan bindiga

Katsina na daga cikin Jihohin yankin arewa maso yammacin Najeriya da suke fama da matsalar hare-haren ‘yan bindiga, lamarin da ya tilastawa dubban mutane tserewa daga muhallansu, inda was uke gudun hijira a sassan jihar ta Katsina, a yayin da wasu kuma suka tsere zuwa cikin Jamhuriyar Nijar.

Rfi Hausa

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan