Fitila: Manyan Abubuwan Da Suka Faru A Duniya A 2021

    315

    Wannan makwon bari mu yi duba da waiwaye kan wasu manyan al’amura da suka faru a shekarar da muka yi bankwana da ita, wato shekarar 2021. Wannan shekara ta zo wa da duniya da matsaloli da dama musamman ga ƙasashe masu tasowa irin Najeriya. Duk da dai cewa annobar Cutar Sarƙewar Numfashi wacce aka fi sani da Corona Virus ko COVID-19, gadar ta shekarar ta yi domin an faro cutar ne tun a shekarar 2019.

    Hoton Ƙwayar Cutar COVID-19

    Wannan annoba ta yi sanadiyyar durƙushewar tattalin arziƙin ƙasashe da dama da sanya gwamnatoci canja akalar tafiyar da mulkinsu.

    Hakazalika, a shekarar ne dai Shugaban Ƙasar Jamus, Angela Merkel ta ajiye mukaminta bayan ƙin sake tsayawa takara da ta yi bayan shafe shekaru 16 tana mulkin ƙasar.

    Tsohuwar Shugabar ta cim ma nasarori da dama ta inda ta saita tattatalin arziƙin ƙasar ta Jamus wadda yanzu a duniya yake kan gaba-gaba, sannan Shugabar ta samar da kyakkyawon tsari da inganta rayuwar ‘yan ƙasar ta Jamus.

    Hakazalika, a shekarar ne dai ‘yan Ƙungiyar Taliban suka dawo mulkin ƙasar Afghanistan bayan shafe shekara 25 da barin kasar Afganistan bayan da Amurka da ƙawayenta suka fatattake su daga mulkin ƙasar.

    Mayaƙan Ƙungiyar Taliban, Afghanistan

    A halin yanzu, ‘yan Taliban suna ƙoƙarin sake kafa wani sabon mulki a Afghanistan duk da dai suna fuskantar ƙalubale da dama, kama daga cikin gida har zuwa ƙasashen waje, hakan ne ya sa ‘yan ƙasar suka fara tserewa zuwa wasu ƙasashe domin neman mafaka.

    Haka kuma, idan muka gangaro zuwa ƙasashen Afirka, ƙasar Sudan ta Arewa ta sake komawa cikin ruɗani, ƙasar da take cikin masassara tun bayan tumɓuke gwamnatin Shugaba Albashir. A watan Oktoba na shekarar ne dai Janar Abdel Fattah Al-Burhan ya yi wa gwamnatin riƙon ƙwarya ta Firaminista, Abdalla Hamdok juyin mulki, inda sojoji suka yi awon gaba da Firaministan tare da ‘yan majalisa fiye da mutum 50.

    Sai dai bayan matsin lamba daga ƙasashen ƙetare tare da zazzafar zanga-zanga daga ‘yan kasar, sojojin sun dawo da Firaministan kan mulkinsa tare da sakin dukkanin waɗanda suka kama. Sai dai jim kaɗan da cim ma yarjejjeniyar, ‘yan ƙasar suka sake dawowa kan titina don gudanar da zanga-zanga kan zargin sojojin da yin baba-kere kan tafiyar da gwamnatin ƙasar. Ko a makwon da muka yi bankwana da shi, an samu labarin rasa rayukan fiye da mutum biyar bayan da sojoji suka bude wa masu zanga-znga wuta.

    A ƙasa Najeriya kuma, kaɗan daga abubuwan da suka faru da suka shafi tsaro, siyasa da tattalin arziƙi.

    Batun hana amfani da kafar sadarwa ta Twitter da Gwamnatin Tarayya ta yi bayan kafar ya goge wani rubutu da Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari ya yi a shafinsa akan ‘yan tada ƙayar baya na yankin Kudu Maso Gabas, wato IPOB. Kwanfanin Twitter dai ya ce rubutun na Shugaba Buhari ya saɓa wa ƙa’idoji da dokokinsa.

    Tambarin Kamfanin Twitter

    Sai dai batun bai yi wa gwamnati daɗi ba, inda take ganin kamar kamfanin na Twitter ya fi ba tsageru dama domin su ruguza ta. Nan take gwamnatin ta bakin Ministan Yaɗa Labarai, Lai Mohammed, ta sanar da dakatar da amfani da kafar. Har kawo yanzu dai Gwamnatin Najeriya ba ta bude kafar ba. Sai dai hakan bai hana wasu ‘yan ƙasar amfani da shafin ba, inda suka samar wa kansu wata hanya ta amfani da shafin wadda gwamnatin ba za ta iya hana su ba.

    Sai mu dawo Arewacin Najeriya, inda matsalar rashin tsaro ta ƙi ci ta ƙi cinyaewa. A jihohi irin su Zamfara, Sakkwato, Katsina da Kaduna al’amarin rashin tsaro kullum ƙara taɓarbarewa yake yi.

    ‘Yan Bindiga

    A shekarar ta 2021 ɗin ne wani ƙasurgumin ɗan bindiga wanda ya yi ƙaurin suna a Arewacin Najeriya , wato Bello Buruji, ya tare wasu matafiya, a jihar Sakkwato, inda ya cinna wa motar da suke ciki wuta, abin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 43. Wannan batu ya girgiza al’umma sosai. Sai dai abin ban-haushi, Shugaba Muhammadu Buhari bai ziyarci al’ummar wannan jiha ba ko ‘yan uwan waɗanda aka ƙone domin yi musu ta’aziya. Sai dai aka gano shi a jihar Legas, inda ya je don halartar bikin ƙaddamar da littafin tarihin abokin siyasarsa, wato Bisi Akande.

    Hakazalika, a 2021 ne ‘yan bindiga suka sace ɗaliban Makarantar Jangebe dake jihar Kebbi inda suka tura su cikin daji. Duk da iyayen ɗaliban sun biya kuɗaɗen fansa masu tsoka, sai da aka shafe kwanaki kafin ‘yan bindigar su sako su.. A wani rahoto da jaridar Vanguard ta buga, ta ce a tsakanin watannin Janairu zuwa Yuni, an yi garkuwa da mutane 2,371. Wannan ƙididdiga ba ta haɗa da waɗanda aka ɗauka a yankunan da ba a samu rahoto ba.

    Ganin yadda wannan al’amari ya ƙi ci ya ƙi cinyewa ta sa Gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari ya shawarci al’ummar jihar ce su ɗauki makamai domin kare kansu. Ya ƙara da cewa ya kamata gwamnati ta tabbata ta yi wa al’umma rijistar makamsu domin su riƙa amfani da su wajen kare kansu daga ‘yan bindigar. Al’umma dai sun daɗe suna kokawa kan halin ko-in-kula da gwamnati take nunawa akan lamarin tsaro a yankin na Arewacin Najeriya. Hukumomi da alhakin kare rayukan al’umma yake a kansu ba sa ɗaukar matakan da suka dace domin kawo ƙarshen rashin tsaro.

    Sai mu yi duba mu ƙarƙare da jihar Kano- Jihar da take ɗaya daga cikin manyan jihohin Najeriya ta fannin kasuwanci da kuma siyasa. A fannin kasuwanci, al’ummar jihar sun koka matuka a shekarar da ta gabata, musamman ‘yan kasuwar dake Kantin Kwari da Ƙofar Wambai, inda gwamnatin jihar take fitar da shaguna akan tituna barkatai.

    ‘Yan kasuwar sun yi kukan cewa hanyoyin da ya kamata a ce ana bi duk gwamnati ta yanka su ta mayarda da su shaguna. Wannnan ne ya sa wasu daga cikin ‘yan kasuwar suka yi zanga-zanga domin nuna fushinsu akan batun. Al’amarin na yanka filayen barkatai ba wai akan kasuwannin kawai ya tsaya ba, har masallatai ma ba su tsira ba, inda rahotanni suka nuna gwamnatin ta yanka filayen masallatai da dama a jihar cikin har da Masallacin Idi da Masallacin Juma’a na Fagge. Yanka filin Masallacin Juma’a na Faggen ne ya sa Shugaban Masallacin, Sheikh Tijjani Bala Kalarawi ya yi murabus.

    Masallacin Juma’a na Fagge, Kano

    A batun siyasa kuwa, an samu tata-ɓurza a jihar ta Kano ba kaɗan ba inda jam’iya mai ci, wato APC take ta samun ƙarin rarrabuwar kai. Masu bibbiyar wannan jarida sun sha karanta yadda muka kawo muku labarin ɓangarori biyu da aka samu a jam’iyar ta APC. Ko a zaɓen shugabannin jam’iyyar na jiha da aka yi, an samu shugabanni guda biyu waɗanda suke iƙirarin shugabancin jam’iyar. Waɗannan ɓangarori sun hada da ɓangaren da Mai Girma Gwamna Ganduje yake jagoranta, wanda yake da Abdullahi Abbas a matsayin shugaban jam’iyya, sai kuma tsagin ‘yan G7 wanda tsohon Gwamna kuma Sana

    Tuni dai akan wannan batu kotu ta tabbatar da zaɓen da aka yi wa Amadu Haruna Zago a matsayin halattacce inda ta rushe zaɓen da tsagin Mai Girma Gwamna ya gudanar.

    Sai dai wani abu mai kama da mi’ara-koma- baya, a kwana kwanan nan an gano Mai Girma Gwamna a gidan tsohon maigidansa a siyasa, wato Rabi’u Musa Kwankwaso, Shugaban Ɗarikar Kwankwasiyya, inda aka jiyo Gwamnan yana cewa akwai yiwuwar sulhuntawa tsakaninsa da tsohon mai gidan nasa. To amma babban abin rikici cikin wannan lamari shi ne yadda magoya bayan kowane ɓangare suka hau kujerar na-ƙi game da sulhu. Koma dai mene ne, za mu jira mu ga abin da zai faru a wannan shekara.

    Turawa Abokai

    RUBUTA AMSA

    Rubuta ra'ayinka
    Rubuta Sunanka a nan