Yadda Sanatocin Najeriya Suka Ƙaurace Wa Zaman Majalisa A 2021

262

Wani bincike ya gano cewa a gaba ɗaya shekarar da ta gabata, wato 2021, sanatocin Najeriya sun yi zaman majalisar sau 66 ne kawai.

Wannan yana nufin sun yi zaman da bai haura wata biyu ba. Ko kuma idan za a yi amfani da kalandar majalisar na zaman majalisa sau uku a sati, za a iya cewa sun yi zaman wata biyar da kwana shida ne kawai.

A halin yanzu ma sanatocin suna hutun mako huɗu don murnar bukukuwan Kirsimeti da na Sabuwar Shekara.

Wannan hutu, kodayake yana da muhimmanci, yana ɗaya daga cikin hutun da Majalisar Dattijai ta tafi a 2021.

Tsakanin 23 ga Fabrairu, lokacin da sanatocin suka dawo daga hutun 2020 zuwa lokacin da suka rufe majalisar ranar 22 ga Disamba, 2021, sun tafi hutu aƙalla sau takwas.

Tsawon hutun da suke tafiya ya kama daga mako ɗaya zuwa mako takwas, ya danganta da dalilin hutun.

Suna tafiya hutun ne ko dai don su yi jimamin rasuwar ɗaya daga cikinsu, murnar wani biki, zuwa tarukan jam’iyyunsu ko kuma su kai ziyarar aiki a matakin kwamitoci.

Zaman majalisa da suka yi sau 66 a 2021, ya nuna cewa ‘yan majalisar ba su cika ƙa’idar zamba majalisa da kundin tsarin mulki ya tanada ba ta kwana 181 a shekara.

Haka kuma a dai 2021 ɗin, sanatocin sun karya wasu daga cikin dokokin Majalisar Dattijan, ta hanyar sauya ranakun da suke zama a mako.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan