Hambararren shugaban Mali Ibrahim Boubacar Keita ya rasu, kamar yadda tsohon ministan shari’a kuma tsohon mai ba shi shawara ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters a ranar Lahadi.
Ya mutu yana da shekara 76.
Har yanzu dai ba a bayyana musabbabin mutuwar ba.
Keita, wanda aka fi sani da IBK, ya jagoranci kasar ta yammacin Afirka daga watan Satumba na 2013 zuwa Agusta 2020, wani lokaci mai cike da tashin hankalin masu ikirarin jihadi.
Sojoji sun yi masa juyin mulki ne bayan shafe watanni ana zanga-zangar kin jinin gwamnati.
Wani tsohon mai ba da shawara ya ce ya mutu a gida a Bamako babban birnin kasar.
Turawa Abokai